1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta yi Allah wadai da rincabewar rikici a Kwango

February 18, 2024

Yayin fada ke kara kazanta a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango a tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen kungiyar M23, Amirka ta yi gargadi ga 'yan tawayen.

https://p.dw.com/p/4cXYj
Dubban mutane na tserewa daga birnin Goma na Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango
Dubban mutane na tserewa daga birnin Goma na Jamhuriyar Dimokradiyyar KwangoHoto: Moses Sawasawa/AP/picture alliance

Gomman sojoji ne da kuma fararen hula suka mutu a rikici sakamakon kazamin fada a tsakanin 'yan tawayen kungiyar M23 da kuma dakarun gwamnatin kasara yammacin birnin Goma.

A cikin sanarwar da ma'aikatar harkokin cikin gida ta Amirka ta fitar, ta bukacin 'yan tawayen da su gaggauta tsagaita bude wuta tare da ficewa daga yankin.

Kana ta zargi kasar Ruwanda da tallafawa 'yan tawayen. Sai dai Ruwandar ta dade ta na musanta wannan zargin. Amirka dai ta bukacin Ruwanda ta cire na'urorin makamai masu linzami na sama da ta jibge a Kwango.