Fargaba a kan rikicin Libiya | Labarai | DW | 17.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fargaba a kan rikicin Libiya

Al'ummomin kasa da kasa na gudanar da taro a birnin Marid na kasar Spain domin shawo kan rikicin siyasar kasar Libiya da ke ci gaba da ta'azzara.

Ministan harkokin kasashen ketare na kasar Spain Jose Manuel Garcia-Margallo ya ja hankalin al'umomin kasa da kasa kan rikicin Libiya wanda ya ce yana iya juyewa zuwa yakin basasa irin na Siriya. Manuel Garcia-Margallo ya yi wannan gargadin ne a Larabar nan yayin taron da ake gudanarwa a kan rikicin siyasar kasar Libiyan a birnin Marid na kasar Spain, inda ya ce har yanzu akwai sauran lokaci da za a iya hana masu tsattsauran ra'ayi su yi jagorancin kasar. Taron dai na samun halaratar jami'an Majalisar Dinkin Duniya da na kungiyar kasashen Larabawa da kuma wakilai daga wasu kasashen duniya 16. A jawabinsa wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Libiyan Bernardino Leon, jaddada bukatar tsagaita wuta a rikicin Libiyan ya yi. Tun bayan da aka kifar da gwamnatin marigayi Mu'ammar Gadhafi kasar ta Libiya ta tsunduma cikin rikici da har yanzu aka gaza shawo kansa.