Faransa za ta yi wa bakin haure rajista | Labarai | DW | 28.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa za ta yi wa bakin haure rajista

Faransa ta bullo shirin yi wa bakin haure rajista a Libiya, a dai dai lokacin da nahiyar Turai ke fuskantar karuwar kwararar bakin da ke shigo masu ta ruwa.

Gwamnatin kasar Faransa ta bijiro da wani shirin yi wa bakin haure rajista a Libiya, a dai dai lokacin da kasahsen Turai ke ci gaba da fuskantar karuwar kwararar bakin da ke shigo masu ta kogin Baharrum.

Shugaba Emmanuel Macron wanda ya sanar da tsara sabon shirin, ya ce za a yi hakan ne cikin makonnin da ke tafe inda za a yi wa masu ketarawan rajistar samun mafaka, amma fa a Afirka. 

Kasar Libiya ta kasance mahadar Turai da Afirka wadda bakin haure ke amfani da ita wajen shigewa ba bisa izni ba. Afirkawa da wasu larabawa ne dai ke ta mutuwa a teku sanadiyar son shiga kasashen na Turai.