1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta gargadi Mali kan sojojin hayan Rasha.

Ramatu Garba Baba
September 21, 2021

Ministar tsaron kasar Faransa Florence Parly ta gargadi gwamnatin Mali kan shirin daukar sojojin haya daga Rasha gudun kada a mayar da kasar saniyar ware.

https://p.dw.com/p/40atr
ECOWAS Westafrikanische Staaten verhängen Sanktionen gegen Mali und Guinea
Hoto: Nipah Dennis/AFP

Faransa ta gargadi Mali kan dauko sojojin haya daga Rasha. Ministar tsaron kasar ta Faransa Florence Parly da ke rangadi a kasashen yankin Sahel, ta ce daukar wannan matakin zai janyo wa Mali koma baya, don kuwa za ta zama saniyar ware a tsakanin kasashen duniya.

Ministar a yayin ganawa da manema labarai, ta ce, bai dace ba, Mali ta dauki wannan matakin, a daidai lokacin da kasashen duniya ke hada karfi da karfe don taimakon kasar da sauran kasashen yankin Sahel yakar 'yan ta'addan da suka hana zaman lafiya da ma ci gaban yankin.

A makon da ya gabata ne, wani rahoto ya rawaito cewa, sabuwar gwamnatin soji a Mali, ta shirya dauko hayar sojoji kimanin (1,000) dubu daya na mayakan kamfanin Wagner da ke Rasha, mayakan da aka jima ana zargi da aikata laifuka na cin zarafin bil'adama.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tafka mahawara, kan matakin Faransa na maido da hedikwatar sojojinta masu yaki da ta’addanci a Sahel daga Mali zuwa Nijar.