Faransa na gudanar da taro a kan Ukraine | Labarai | DW | 23.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa na gudanar da taro a kan Ukraine

Ministocin harkokin waje na ƙasashen Rasha da Ukraine da Faransa da kuma Jamus na tattaunwa a birin Paris na Faransa a kan rikicin na Ukraine.

Ministocin na waiwaye adon tafiya ne a game da inda aka kwana dangane da aiwatar da yarjejeniyar MINSK a Ukraine.Wannan saduwa dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da Ƙungiyar Tarrayar Turai,ta amince da wani ƙudirin tsawaita takunkumin karya tattalin arziki ga Rasha saboda rawar da take takawa a yaƙin da ake yi a gabashin Ukraine.

An dai ci gaba da gwabza yaƙi tsakanin dakarun gwamatin da na 'yan aware a gabashin ƙasar duk da yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar da aka cimma a watanni huɗun da suka gabata.