Faransa da Madagaska na jan-in-jan kan ikon tsibirin Eparses
July 4, 2025
Faransa ta sake jaddada ikon da take da shi a kan tsibirin Eparses da take takaddama a kai da Madagaska, wanda ke da dimbin hallitun ruwa, kuma ya kai grman kilometa bakwai murabba'i. A yayin wani taron hadin gwiwa da suka gudanar a birnin Paris, ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noël Barrot da takwaransa na Madagaska Rafaravavitafika Rasata suka ce har yanzu kasashen biyu na ja in ja kan wanda ya mallaki tsibirin, ba tare da cimma gagarumin ci gaba kan yadda za a tafiyar da shi ba.
Duk da cewar Madagaska na da'awar mallakar wannan tsibiri, amma sassan biyu sun nuna aniyar gudanar da aikin hadin gwiwa kan batutuwan da suka shafi halittu da binciken kimiyya da tattalin arzikin da tsaron teku. Sai dai, Madagaska ta bukaci a biya ta diyya kan barnar da Faransa ta yi wa tsibirin. Amma sassan biyu ba su bayyana aniyar shigar da kara kotun kasa da kasa don tantance kasar da ta mallakin tsirin Eparse ba.