1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin adawa da gwamnatin Faransa

March 24, 2023

Ma’aikata a Faransa na ci gaba da zanga-zangar adawa da matakin gwamnatin Shugaba Emmanuel Macron da ta kara yawan shekarun ritaya a kasar.

https://p.dw.com/p/4PDsD
Masu zanga zanga a Paris
Masu zanga zanga a ParisHoto: Bob Edme/AP/picture alliance

Masu zanga-zangar dai na taho mu gama da jami’an tsaro tare ma da kone-kone duk dai saboda turje wa wannan matsayi na gwamnati. 

Zanga-zangar ta yi matukar kamari a Faransa inda sannu a hankali ta yi zafi Paris babban binrin kasar, inda masu bore ke ta arangama da jami'an tsaro.

Wannan dai mataki ne suka dauka domin bijire wa tsarin sauye-sauye na fansho da Shugaba Emmanuel Macron ya bijiro da su, inda daga ciki har da karin wasu shekaru biyu kan shekaru 62 da aka sani kafin ma'aikaci ya yi ritaya a kasar.

Ana dai kallon hakan a matsayin kokari na gwamnatin ta Faransa na kara wa kanta lokacin da zai ba ta damar tattara kudaden karo-karon na fansho, saboda karancin kudade da take ciki.

Rahotanni sun tabbatar da cewa arangamar tsakanin jami'an tsaro da masu zaga-zangar, ta jikkata jami'an tsaro da dama.

Shugaba Emmanuel Macron
Shugaba Emmanuel MacronHoto: Ludovic Marin/dpa/picture alliance

An kuma tsare da dama daga cikin fararen hula da aka kama a wurare daban-daban a fadin kasar.

Wannan wata mata ce da ke cikin masu adawa da matakin, kuma aikinta shi ne kula da kananan yara a birnin Paris.

"Ba mu yarda da karin shekaru biyu da aka ce an yi a kan shekaru 62 da dama ake kai ba. Ba ma ganin kanmu a matsayin wadanda za su ci gaba da aikin nan har na wasu shekaru biyu nan gaba. Mata ne mu, hakan na nufin ke nan zan kai sama da shekaru 64 ma. Don haka mu ba u amince ba."

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa dai ya yi alkawarin yi wa kasar abubuwa biyu manya, wadanda suka hada da sauyata ta fuskar ci gaba da kuma hada kan al'umarta, abin da wasu ke ganin bai dauki hanyar samar da su ba.

Yanzu dai sama da mutum miliyan guda ne ke wannan bore, kuma kungiyoyin ma'aikata sun yi kiran a fadada zanga-zangar zuwa dukkanin sassan kasar a ranar Talata, abin da zai ci karo da wata ziyarar farko da Sarkin Ingila Charles na uku zai kai Faransar.

Bisa tsari dai a ranar Lahadi ne Sarki Charles na uku tare da rakiyar uwargidansa Sarauniya Camilla za su ziyarci kasar. Kuma wannan ce ziyararsa ta farko da za iyi a Faransa a matsayin Sarkin Ingila.

Kungiyoyin na ci gaba da zargin gwamnati da sanya kasar a halin da take ciki, tare da yin kira ga ma'aikata da su ci gaba da bijire wa sauye-sauyen tsarin fansho da Shugaba Macron ya bjiro da su.

Wasu shugabannin kamfanoni ma a Faransar, na goyon bayan ma'aikatansu a wannan fafutika, inda guda daga cikin jagororin kamfanin sarrafa makamashin mai na Total Alexis Antonioli ke martini kan abubuwan da ‘yan sandan kwantar da tarzoma musamman suka yi.

Zanga zangar adawa da gwamnati
Zanga zangar adawa da gwamnatiHoto: Jeremias Gonzalez/AP Photo/picture alliance

"A gaskiya ‘yan sanda sun kutsa ta hanyar tarwatsa tare da mamaye mashigar kamfaninmu. Babban abu dai a nan mu ba za mu hana su zuwa aiki ba. Abun da muke fadi a nan shi ne kamata ya yi a nemi izinin yin abin da aka yi, ammam abin da aka yi bai bi wannan tsarin ba. Da dama daga cikin abubuwan da ake yi a wannan dambarwa musamman daga mahukunta, na taba ‘yancin mutane na fadar albarkacin bakinsu.”

Da ma dai a ranar Juma'ar da ta gabata ne aka fara yajin aiki na kamfanonin tace man fetur a kasar ta Faransa, abin da ke shafar aikin tace mai da kamfanonin Faransa ke yi, inda gidajen sayar da mai ke fama da karancin makamashin saida wa jama'a.

Haka ma akwai yadda zanga-zangar da yajin aikin ke shafar su ayyukan da kamfanonin sarrafa iskar gas ke yi ta a karshe ke hawa kan duk wani aiki na samar da makashin ga al'umar kasar da ma ketare.