Fara ibadar Azumin Ramadan a fadin duniya | Labarai | DW | 17.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fara ibadar Azumin Ramadan a fadin duniya

Mahukunta a Saudiyya da Iran da Indonesiya da sauran wasu kasashen na Musulmi sun bayyana cewa da zarar an ga jinjirin watan Ramadhana a fara azumi Alhamis.

Indonesien Lesende Muslima

Musulmi na karatun Qur'ani


Musulmi a fadin duniya na daf da fara ibadar watan Azumin Ramadan, ibadar da akan fara tun daga billowar alfijir zuwa faduwar rana tsawon wata guda.

Mahukunta a kasashen Saudiyya da Iran da Indonesiya da sauran wasu kasashen na Musulmi sun bayyana cewa da zarar an ga jinjirin watan Ramadan a yammacin na Laraban nan za a tashi da azumi a ranar Alhamis.

Wannan wata dai mai tsarki na Ramadan a shi ne al'ummar Musulmin duniya ke kara azama wajen ibada dan neman kusanci da mahalicci Allah. A kowace rana cikin watan da zarar rana ta fadi Musulmi kan bude baki da ruwa ko dabinu ko dai abin da ya sauwaka.