Falasdinu na son dauketa a matsayin kasa | Labarai | DW | 22.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Falasdinu na son dauketa a matsayin kasa

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya yi wani zama da ministocin harkokin wajen kasashen EU inda ya bukacesu da su gaggauta amincewa da Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Shugaba Abbas ya ce Falasdinu ta dauki EU a matsayin aminiya, wannan ne ma ya sanya ya ce za su cigaba da aiki da ita wajen ganin zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya ya wanzu, kan haka ne ma ya ce lokaci ya yi da za a amince da kasarsu a matsayin kasa kamar yadda aka dauki sauran kasashen duniya.

Wannan zantawar ta Abbas da EU din dai na zuwa ne daidai lokacin da mataimakin shugaban Amirka Mike Pence ke wata ziyara a Isra'ila inda ya shadiawa majalisar dokokin kasar cewar a karshen shekarar 2019 ne Amirka za ta maida ofishin jakadancinta zuwa birnin Kudus, matakin da Falasdinu ke adawa da shi.