Fafutukar yaƙi da hamada a Nijar | Zamantakewa | DW | 22.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Fafutukar yaƙi da hamada a Nijar

Ƙungiyar EU na ba da horo ga jami'an ƙungiyoyin farar hulla da na kafofin yaɗa labarai, domi ɗaukar matakkan yaƙi da barazanar mamayewar hamada.

Ƙungyiyar tarayyar Turai tare da haɗin gwiwar wasu manyan ƙungiyoyin ne ke ƙaddamar da wannan babban aiki na yin rigakafi ga gurgusowar hamada a Nijar.

A ƙasa da shekaru goma da suka gabata ƙasar ta Nijar ta yi fama da mumunar yanayi na samun koma baya a sha'anin noma da kiwo, duk kuwa hakan na da nasaba ne da gurgusowar hamadar. Wannan shi ya sa ƙasahen duniya suka tashi tsaye haiƙan wajen faɗakar da wakilai na ƙungiyoyi daban-daban domin su kawo tasu gundunmawa domin yin riga kafi.