Fafutukar samar da zama lafiya a Kaduna | Zamantakewa | DW | 25.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Fafutukar samar da zama lafiya a Kaduna

An cimma wata yarjejeniyar samar da zaman lafiya tsakanin dukkanin kabilun yankin Zangon Kataf da ke a yankin kudancin Kaduna.

Mun yi amfani da tsohon hoto na wani harin bam da aka kai a Kaduna

Mun yi amfani da tsohon hoto na wani harin bam da aka kai a Kaduna

 An cimma wata yarjejeniyar samar da dorewar zaman lafiya a tsakanin dukkanin kabilun karamar hukumar Zangon Kataf na yankin kudancin Kaduna, wadanda suka hada da Hausawa da Fulani da sauran kananan kabilun yankunan kudancin Kaduna. Bayan Tashe-tashen hankula da kashe-kashen rayuka da suka samu asili tun shekaru da dama, sarkin kabilar Atiyaf Dominic Yahaya ne dai ya gayaci wannan taro domin tattaunawa tsakanin kabilun domin samar da zaman lafiya .

Gargadi ga al'umma a game da tabbatar da zaman lafiya tsakaninn mabiya addinai da sauran su

Tsohon hoto na harin da aka kai a kan wata coci a Kaduna

Tsohon hoto na harin da aka kai a kan wata coci a Kaduna

Masarautar ta gargadi al'ummar a kan daukar mataki a kan duk wasu tashe-tashen hankula domin samun hadin kai da zaman lafiya a tsakanin dukkanin kabilun yankin kudancin Kadunan. Hanyoyin samar da zaman lafiya dabam-dabam ne dai aka tattauna bayan kashe-kashe rayukan da suka tilasta wa darurruwan jama'a yin gudun hijira. Bugu da kari kwararru da jakadun zaman lafiya da suka fito daga wasu jihohi makwapta sun bukaci ganin an dauki dukkanin matakan da suka dace na kawo karshen zubar da jini a wannan yankin .

Gudumowar matasa wajen kyautatuwar zaman lafiya a Kaduna

Matasa da sauran mazauna garin sun ba da gudunmowar su domin kawo zaman lafiya da tabbatar da hadin kan al'umma.
Tuni da gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya nuna jin dadin sa wanda ya ce yunkurin zai kafa dambar zaman lafiya mai dorewa a kudancin Kaduna inda jama'a za su rika yin walwala ba tare da wani fargaba ba.

Sauti da bidiyo akan labarin