Fafaroma ya shawarci EU kan bakin haure | Labarai | DW | 06.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fafaroma ya shawarci EU kan bakin haure

Shugaban darikar katolika na duniya Fafaroma Francis, ya bukaci kasashen nahiyar Turai da su cire shingen da suka yi domin hana bakin haure shigowa Turai.

Fafaroma Francis da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a fadar Vatican

Fafaroma Francis da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a fadar Vatican

Fafaroma ya yi wannan kira ne a yayin da aka karramashi da kyautar Karl da wata kungiya a birnin Aachen da ke yammacin Jamus ke bayarwa ga mutanen da suka cancanta a Turai da kuma wadanda suka taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiya.

A yayin bayar da wannan kyauta da aka fara ba da ita a shekara ta 1950 dai mambobi da shugabannin kungiyar Tarayyar Turai na halarta domin karrama wanda ya samu nasarar lashe kyautar. Da yake jawabi a fadarsa ta Vatican gaban jiga-jigan kasashen Turai da suka hadar da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da sauran shugabannin kungiyar Tarayyar Turan EU, mai shekaru 79 a duniya Fafaroma ya ce in har ana son bunkasar tattalin arziki a Turai to ko ya zamo wajibi a samar wa da matasa ayyukan yi, ta hanyar fito da matakan bunkasa jin dadin al'umma da ma tattalin arziki da zai taimaki mutane da dama yana mai cewa:

"Ina mafarkin Turai da matasa za su shaki iskar 'yanci da gaskiya tsagwaronta, Ina mafarkin Turai da matasa za su samu soyayya da rayuwa mai sauki, ba Turai da matasa za su fuskanci wahalar rayuwa da rashin aikin yi ba."