Faduwar jirgin sama ya kashe mutane 37 a Iran | Labarai | DW | 27.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faduwar jirgin sama ya kashe mutane 37 a Iran

Wani jirgin dakarun Sojin Iran ya yi hatsari a filin saukan jiragen sama dake birnin Tehran,inda ya kashe mutane 37 dake ciki,da suka hadar da jamian kare juyin juwuya halin Islama guda 31,da maaikatan jirgin guda 6.Kafofin yada labarun kasar Iran din sun sanar dacewa jirgin saman kirar Antanov 74,ya fadi ne da safiyar yau jim kadan da tashin sa.Mutum guda ne kadai ya tsira da ransa,wanda a halin yanzu yake jinya a asibiti.Rundunar jamian kare juyin juya halin kasar dai,na zama reshen rundunar sojin wannan kasa ta janhuriyar