1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fadan jami'an tsaro da 'yan Shi'a

Yusuf Bala Nayaya
October 30, 2018

A ranar Litinin dai sojoji a birnin na Abuja sun bude wuta ga 'yan kungiyar ta IMN da ke zama 'yan Shi'a wadanda ke fafutukar ganin an saki jagoransu da ke hannun mahukunta a Najeriyar.

https://p.dw.com/p/37O7h
Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Hoto: picture alliance/AP Photo/M. Giginyu

Jami'an 'yan sanda a Najeriya sun harba alburusai da hayaki mai sa hawaye ga 'yan Shi'a da ke zanga-zanga a birnin Abuja fadar gwamnatin Najeriya kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana a wannan Talata.

A ranar Litinin dai sojoji a birnin na Abuja sun bude wuta ga 'yan kungiyar ta IMN wadanda ke fafutukar ganin an saki jagoransu da ke hannun mahukunta a Najeriyar.

Masu zanga-zangar dai ta 'yan Shi'a a Najeriya sun bayyana cewa a harbin da sojojin suka yi mambobinsu sun halaka mutane 18 a ranar Litinin ko da yake sojojin na cewa mutum hudu ne suka rasu yayin da sojoji hudu suka samu raunika.