1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU zata tattauna kan sabuwar dokar kasar Hungary

June 24, 2021

Takaddama kan sabuwar dokar kasar Hungary ta haramta tallata abun da ya shafi auren jinsi a makarantu ka iya zama jigon taron koli na shugabannin kungiyar Tarayyar Turai.

https://p.dw.com/p/3vTHx
BdTD Fußball EM Deutschland Ungarn Regenbogen Stadion
Hoto: Michael Sohn/AP Photo/picture alliance

A cewar wani jami'in kungiyar, batun cecekuce kan sabuwar dokar kasar Hangary din wani babban abun dubawa ne a taron da zai gudana a ranakun Alhamis da Juma'a. Batun dai na zama na gaba-gaba a siyasar Turai a wannan makon biyo bayan matakin Hukumar Kwallon Kafa ta Turai na haramta shirin haskaka filin wasan Munich cikin launukan da ke alamta auren jinsi yayin wasa tsakanin Jamus da kasar Hungary a ranar Laraba.

Fiye da rabin kasashen dake kungiyar ta EU da suka hada da Jamus da Faransa da Italiya da kuma Spaniya ne suka yi wa kasar ta Hungary rubdugu kan sabuwar dokar tare da yin kira kungiyar ta dau mataki da a ganinsu take hakkin ne.

Kazalika kuma ana ganin cewa wannan taron ka iya zama na karshe da shugabar gwamnatin Jamus zata halarta a matsayinta ta shugaba a kungiyar ta EU.