EU zata kafa sansani a Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 06.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU zata kafa sansani a Afirka ta Tsakiya

Ministocin harkokin wajen kasashen Turai sun amince da kirkirar sansanin horar da sojoji a yankunan Afirka da ke fama da rikice-rikice.

Kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun  amince da bude wata karamar cibiya don horar da sojoji a kasashen waje a wani mataki da Faransa da Italiya suke fatan ya zama shimfida ga yunkuri tanadin hedikwatar tsaro ta kungiyar tarayyar Turai. Kasashen Faransa da Italiya na ganin wannan yunkuri zai taimaka wajen inganta tsaro a hedikwatar tarayyar Turai.

kungiyar tarayyar Turan na neman daidaita karfin tattalin arziki ta da kokarin magance ta'addanci ko kuma barazanar kasar Rasha da yin amfani da jami'an kwantar da tarzoma don dawo da zaman lafiya a iyakokin kasashen tarayyar Turai a halin yanzu. Shi dai wannan sabon tsari  zai dauki alhakin horar da dakarun kungiyar a kasar Mali da Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da kuma somaliya, bangare daya ya kunshi hadin gwiwa wajen saye da bayar da aron tankokin yaki.