EU za ta rage dogaro kan makamashi daga Rasha | Siyasa | DW | 21.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

EU za ta rage dogaro kan makamashi daga Rasha

A karshen taron kolin da suka yi a Brussels shugabannin EU sun fadada takunkumai kan Rasha sannan sun amince da matakin farko na daukar Ukraine cikin kungiyar.

A rana ta biyu kuma ta karshe a taron kolinsu na birnin Brussels shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Turai sun amince su hanzarta hankoron samun tabbaci na makamashi, suna masu cewa matakin da Rasha ta dauka na hade yankin Kirimiya ya sa sun yanke kudurin rage dogaro kan mai da kuma iskar gas daga Rasha. Da ma tun farko a wannan Jumma'a kungiyar EU ta yi maraba da Ukraine a cikin jerin kasashen yamma, inda ta sanya hannu kan bangaren siyasa na yarjejeniyar shigar da Ukraine din cikin EU.

Rana ta tarihi ga Turai

Tarayyar Turan ta sanya hannu kan wannan yarjejeniya ta tarihi a daidai lokacin da a hukumance Rasha ta kammala karbar yankin Kirimiya. Shugaban EU Hermann Van Rompuy ya fada wa firaministan rikon kwaryar Ukraine Arseniy Yatsenyuk cewa sanya hannu kan yarjejeniyar ta nuna muhimmancin da bangarorin biyu suka ba wa wannan dangantaka da kuma kudurin fadada ta. Ya ce EU tana goyon bayan Ukraine dari bisa dari yana mai daukar alkawarin ba da taimako don farfado da tattalin arzikin Ukraine. Shi ma a nasa martanin bayan shugabannin EU 28 sun sanya hannu kan yarjejeniyar firanministan Ukraine Arseniy Yatsenyuk cewa yayi.

"Wannan rana ce ta tarihi ga kasa ta, mun kuma yi imani rana ce ta tarihi ga Turai baki daya. Muna son mu zama wani bangare na iyalin Turai, kuma wannan shi ne babban matakin farko na cimma burin zama cikakkiyar memba a kungiyar EU."

A wani bikin da ya gudana a birnin Mosko kuwa shugaba Vladimir Putin ya rattaba hannu kan ne yarjeniyoyin da suka mayar da Kirimiya wani yanki na Rasha, inda ya taya al'ummar yankin da ma Rashawa gaba daya murnar wannan rana.

Shigar da yankin na Kirimiya bayan kuri'ar raba gardamar ranar Lahadi da ta sha suka daga Amirka da kuma kasashen EU, sassan biyu sun sanya wa Rasha takunkumai. Ita kuma Rasha ta mayar da martani inda ta sanya takunkumai kan wasu jami'an Amirka ciki har da 'yan siyasar kasar.

Karin takunkumai kan Rashawa

Bayan doguwar tattaunawa a birnin Brussels shugabannin EU su fadada takunkuman a kan karin Rashawa 12 inda suka sanya musu haramcin tafiye tafiye da kuma dora hannu kan kadarorinsu. Yanzu yawan Rashawan da takunkuman ke kansu ya kai 33. Sai dai shugaban tsibirin Cyprus Nicos Anastasiades ya yi kashedi da a yi takatsantsan ka da wuce gona da iri bisa matakan da ake dauka.

"Mun yi kadan kwarai da gaske har da za mu iya daukar wani mataki kan Rasha. Dole ne dai mu ba da la'akari da kudurorinmu. Amma dole ne kuma mu guji daukar wasu matakai da za su illa ga tattalin arzikinmu."

Shugabannin na EU sun kuma amince da bukatar gaggauta shirye-shiryen rage yawa dogaro da kungiyar ke yi a kan makamashi musamman daga Rasha, da ke bi ta Ukraine zuwa kasashen kungiyar. Daukacin kasashen EU sun dogara da makamashi daga Rasha, amma wasu kasashen irinsu Hungary da Bulgariya da suka dogaro kan Rashan ba sa son an sanya takunkumin karya tattalin arziki gaba daya. Da ma tun gabanin taron shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce za a duba batun karin takunkumin ne idan halin da ake ciki ya ta'azzara.

"Mun nuna a fili cewa a shirye muke mu shiga mataki na uku na takunkumi wato na karya tattalin arziki, idan halin da ake ciki game da Ukraine ya yi muni."

Kawo yanzu yunkurin EU na fadada wuraren da ta take samun makamashi biyo bayan rage yawansa da Rasha ke tura wa Ukraine a shekarun 2006 da 2009, ya ci-tura.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh

Sauti da bidiyo akan labarin