EU za ta aika martani mai tsauri kan rikicin Ukraine | Labarai | DW | 04.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta aika martani mai tsauri kan rikicin Ukraine

Hakan dai ya zo bayan da ake ci gaba da fada a gashin kasar ta Ukraine, abin da ke bazarana ga yarjejeniyar da aka cimma a Minsk, inda ake zargin Rasha da rashin jan kunnen 'yan bindigan

A cewar shugabannin kasashen yamma, duk wani yaunkurin sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta a gabashin Ukraine, to kuwa kasar Rasha za a dorawa alhakin domin ita kawai ke iya jan kunnen yan aware dake neman ballewa.

Shugabannin kasashen Amirka da Jamus da Faransa da Birtaniya da Italiya dama jagoran Tarayyar Turai wato Donald Tusk, sun yi muhawara kan yadda za a karfafa sa ido kan batun, da ma batun janye manyan makamai a gabashin na Ukraine.

Kamar dai yadda kamfanin labaran Faransa AFP ya ruwaito, shugabannin sun amince su bayar da cikakken goyon bayansu kan tsagaita wuta da aka yi a birnin Misnk na kasar Belarus, a ranar 12 ga watan jiya wato Fabrairu.

Koda yake shugabannin na kasashen Yamma, ba su fadi abin da ka iya kasancewa idan aka karya wannan yarjejeniyar ba, sun dai nuna yiwuwar karin takunkumi kan Moscow da su ka yi zargin ta na taimakawa 'yan tawaye masu goyon bayan Rasha a yakin.