1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafi ga wasu kasashen Afrika

Binta Aliyu Zurmi
June 21, 2022

EU za ta bada tallafi ga wasu kasashe matalauta a Afirka da wasu a yankin Caribbean don rage radadin karancin abinci da yakin Ukraine ya janyo ga duniya.

https://p.dw.com/p/4D0so
Symbolbild Ukraine EU Beitritt
Hoto: Valeria Mongelli/Zumapress/dpa/picture alliance

A kokarin tallafawa kasashe matalauta rage radadin da yakin da Rasha ke yi a Ukraine ya janyo wa duniya a fanni daban-daban. Kungiyar tarayyar Turai ta yi alkawarin karin tallafi na yuro miliyan 600 ga wasu kasashen Afirka da kuma wasu a yankin Caribbean

Shugabar hukumar gudanarwar ta EU Ursula von der Leyen ta ce illar da wannan yaki na Ukraine ke haifar wa duniya bai tsaya a kan al'ummar kasar da ma kasar kawai ba, kasashen masu karamin karfi na shan radadin wannan yaki matuka. 

Daga cikin tallafin da aka ware, yuro miliyan 150 zai je ga kasashen da ke matukar bukata a nahiyar Afirka, yayin da yuro miliyan 350 za a bai wa wasu kasashen yankin Caribbean domin tallafa musu a karancin abinci da suke fama gami da kokarin farfado da tattalin arzikin kasar.

Kasashen yamma da Ukraine na ci gaba da dora alhakin halin da duniya ke ciki kacokam a kan mahukuntan Moscow.

A jiya litinin babban jami'in harkokin kasashen ketare na EU Josep Borrel ya ce hana fidda hatsi da ke jibge a tashoshin ruwan Ukraine da Rasha ke ci gaba da yi laifuka ne na yaki.