EU ta yi tir da tashe-tashen hankula a Kwango | Labarai | DW | 17.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta yi tir da tashe-tashen hankula a Kwango

EU ta yi tir da tashe-tashen hankula a Kwango sannan ta yi barazanar sanya wa gwamnatin Kabila takunkumai.

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta yi barazanar kakaba wa gwamnatin Kwango karkashin Shugaba Joseph Kabila takunkumai saboda tashe-tashen hankula da suka barke a kasar. A cikin wani kuduri da ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar EU suka zartas sun ce kungiyar za ta yi amfani da dukkan hanyoyin da suka wajaba don daukar matakai kan masu yi wa kokarin warware rikicin cikin lumana zagon kasa. Yanzu haka babbar jami'ar da ke kula da harkokin wajen EU Federica Mogherini za ta fara shirye-shirye kan matakan jan kune da za a dauka kan gwamnatin Kwango. A makonnin da suka wuce an yi ta samun munanan tashe-tashen hankula a kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, musamman saboda dage lokacin gudanar da zaben shugaban kasa a watan Nuwamba mai zuwa. 'Yan adawa na zargin Shugaba Kabila da son darewa kan mulki har zuwa karshen shekarar 2018. A ranar Lahadi hadin gwiwar jam'iyyun da ke mulki a kasar da kuma wani bangare na 'yan adawa suka cimma matsaya ta dage lokacin zaben ya zuwa watan Afirilu na 2018.