EU ta jinjina wa Amurka da Iran kan amincewa da yarjejeniya
June 15, 2026
Firaministan Pakistan da ke shiga tsakani Shehbaz Sharif ya sanar da cewa Iran ta amince da sabon daftarin yarjejeniyar tsagaita bude wuta, wanda zai kawo karshen musayar makamai masu linzami har ma da luguden bama-bamai da Isra'ila ke yi a Lebanon.
Karin bayani:Amurka da Iran sun amince da yarjejeniyar sulhu
Firaministan ya sanar da hakan a shafinsa na X, inda ya kara da cewa za a gudanar da kwarya-kwayar bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Yunin 2026 a birnin Geneva na Switzerland. Sharif ya kuma bukaci dukkan bangarorin biyu da su ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu a makonni masu zuwa gabanin taron na birnin Geneva.
Karin bayani:Amurka da Iran na ci gaba da musayar makamai masu linzami
Tun da fari dai Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa suna dab da cimma yarjejeniya da Iran, ciki har da bude mashigar ruwa ta Hormuz ga kasashen duniya.
A nata bangaren, EU ta jinjina wa Amurka da Iran wajen amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya a yakin da aka tafka asara na biliyoyin daloli. Kungiyar Tarayyar Turai ta kuma sanar da cewa kofarta a bude yake wajen ci gaba da ba da gudummuwa wajen tabbatar da zaman lafiya ta dindindin a yankin Gabas ta Tsakiya.