EU ta gargadi Rasha da Amurka kan makamai | Labarai | DW | 05.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta gargadi Rasha da Amurka kan makamai

Jami'ar diplomasiyyar Kungiyar Tarayyar Turai Federica Mogherini ta yi kira ga kasashen Rasha da Amurka, da su taimaka wajen kare yarjejeniyar kula da makaman yakin cacar baka.

Washington ta yi barazanar ficewa daga yarjejeniyar da aka cimma kan makaman nukiliya mai matsakaicin zango a shekara ta 1987, idan har Moscow bata janye  batun shirinta na sabon makami mai linzami da ke barazanar haifar da wani babi na gasar makamai ba.

Mogherini ta jaddada bukatar ceton wannan yarjejeniya, tare da gargadin cewar Turai ba ta muradin sake zama filin daga na manyan kasashe masu fada a ji a duniya, kamar yadda lamarin ya kasance lokacin yakin cacar baka a baya.