EU ta gargadi Birtaniya ta gaggauta biyan bashi | Labarai | DW | 12.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta gargadi Birtaniya ta gaggauta biyan bashi

Wakilin Kungiyar Tarayyar Turai a tattaunawa kan ficewar Birtaniya daga EU ya gargadi kasar da ta biya kudaden bashin da kungiyar da ke wuyanta cikin gaggawa.

Wakilin Kungiyar Tarayyar Turai a kwamitin tattauna matakan aiwatar da shirin ficewar Birtaniya daga kungiyar ta EU Michel Barnier ya yi gargadin cewa lokaci na kara kuracewa a game da batun tattaunawar da ake kan kudaden da Birtaniya za ta biya ga kasashen Turan bayan kammala aiwatar da matakin ficewar tata daga cikin Kungiyar ta EU. Michel Barnier ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron manema labarai a yau a birnin Brussels:

"Ya kamata Birtaniya ta san nauyin da ke a wuyanta na biyan kudaden da ya kamata ta zuba wa kungiyar ta EU a loakcin da take cikinta da wadanda  ko wace kasa ta kungiyar ke zubawa a ko wace shekara"


Kalaman wakilin Kungiyar ta turai a tattauna batun ficewar Birtaniyar daga Kungiyar ta EU na matsayin martani ga kalaman ministan harakokin wajen Birtaniya Boris Johson wanda a jiya Talata a gaban majalisar dokokin Birtaniyar ya bayyana cewa shugabannin Turan za su ko yi dogon jira kafin Birtaniyar ta zuba wadannan kudade da yawansu ya kan na gomma biliyoyin Euro.