EU ta dauki mataki kan sauyin yanayi | Labarai | DW | 24.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta dauki mataki kan sauyin yanayi

Shugabannin Ƙungiyar EU sun amince da rage yawan gurbatacciyar iskar makamashin da ake fitarwa ta "Greenhouse gas emissions" a baki dayan ƙasashen ƙungiyar 28.

Ƙungiyar ta Tarayyar Turai ta amince da rage yawan gurbatacciyar iskar da kaso 40 cikin 100 daga yanzu zuwa shekara ta 2030. Herman Von Rompuy shi ne shugaban majalisar ƙungiyar kuma a ƙarshen taron ya bayyana cewar sun yi aiki tukuru kafin su kai ga cimma yarjejeniyar, ya ce hakan ya buɗe sabon babi a harkar sauyin yanayi da kuma makamashi ga EU. Makasudin cimma wannan yarjejeniya dai shi ne yaƙi da sauyin yanayi da kuma zama abin koyi gabanin babban taro kan sauyin yanayi na duniya da za a gudanar a shekara mai zuwa ta 2015. Kungiyar ta EU dai ita ce ta farko a cikin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki da ta amince da rage yawan gurbatacciyar iskar gabanin wa'adin rageta na nan da shekara ta 2020.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane