EU ta damu da sabon matakin Isra'ila
July 19, 2018Talla
Kungiyar Tarayyar Turai wato EU ta bayyana damuwa kan matakin da majalisar dokokin Isra'ila ta dauka na bayyana cewa Yahudawa ne kadai ke da cikakken 'yancin dan kasa.
A cewar kungiyar ta EU, matakin wata gagarumar matsala ce ga shirin samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da kuma Falasdinu.
Da safiyar wannan Alhamis ne dai Isra'ilar ta amince da dokar, bayan shafe watanni ana ta tabka turanci a kanta.
Tuni dai larabawa marasa rinjaye suka soki matakin, suna mai bayyana shi da wariya karara.
Dokar ta kuma soke amfani da harshen larabci a matsayin harshe da ake amfani da shi a hukumance
Larabawa dai na matsayin kashi 20% na Isra'ilar mai yawan mutum miliyan tara.