1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta rage amfani da makamashin Gas

Abdullahi Tanko Bala
July 26, 2022

Kasashen kungiyar tarayyar Turai EU sun amince da yarjejeniya ta rage amfani da makamashin gas da kimanin kashi 15 cikin dari da kuma rage dogaro kan makamashin daga Rasha.

https://p.dw.com/p/4EgHn
Symbolbild Gas
Hoto: Janek Skarzynski/AFP/Getty Images

Babban kamfanin makamashin gas na Rasha Gazprom ya sanar da cewa daga wannan Larabar zai rage yawan makamashin da yake sayar wa kasashen Turai, lamarin da ke barazana ga kasashe kamar Jamus wadda ta dogara sosai akan Moscow wajen samun makamashin da ta ke amfani da shi a masana'antunta.

Kasashe 27 mambobin kungiyar tarayyar Turai EU wadanda suka sanya wa Rasha takunkumin tattalin arziki domin hukunta ta saboda mamayar da ta yi wa Ukraine, sun amince da matakin rage amfani da gas din da kuma raba nauyin karancin makamashin a tsakaninsu.

Matakin dai na daga cikin dabarun da za su dauka na yin tsimin makamashi gabanin lokacin sanyin hunturu idan Rasha ta katse samar musu da makamashin na gas.