EU: Samar da makoma mai kyau ba Brexit ba
April 16, 2019Talla
Jean-Claude Juncker ya shaidawa majalisar Turan cewa a yanzu kungiyar tarayyar Turai na iya mayar da hankalinta kan shatawa kanta kyakkyawar makoma kasancewar Birtaniya za ta dauki dogon lokaci kafin ta shawarta ficewa daga kungiyar.
Juncker ya shaiadawa shugabannin kasashe 28 na kungiyar ta EU cewa ficewar Birtaniya ba shine makomar su ba a saboda haka bai kamata batun ficewar ta Birtaniya ta kawo musu wani tsaiko ba.
Ya yi tsokaci kan muhimman abubuwan da ke gaban kungiyar ta suka hada da batun kasafin kudi da cinikayya tsakanin kasa da kasa da kuma zaben sabbin shugabanin kungiyar.