EU na tunanin kafa wata runduna
December 15, 2015Talla
Rundunar za ta kula da tsaron iyakokin nahiyar Turai da kuma gaɓar tekun inda har an amince da shawarar.Ƙungiyar ta Eu ta ce kusan mutane miliyan ɗaya da rabi suka tsallaka kan iyakokin na Turai ba kan ƙaida ba tun farkon watan Janeru na wannan shekara akasarinsu 'yan ciranin waɗanda ba a yin rejistansu ba.
Abin da ya sa wasu ƙasashen kamar su Jamus da Austriya tuni suka soma gudanar da bincike na wucin gadi a kan iyakokinsu.