EU na son warware rikicinta da Amirka | Labarai | DW | 22.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU na son warware rikicinta da Amirka

Kungiyar Trayyar Turai ta EU ta ce tana fatan samun daidato kan rashin jituwar da ke akwai tsakaninta da Amirka ta fuskar cinikayya a lokacin taron kasashen G7 a karshen mako wanda za a yi a Faransa.

Wani babban jami'in EU din ne ya ambata hakan, inda ya kara da cewar rikici na kasuwanci tsakanin EU da Amirka ba zai haifar da komai illa dakile cigaban tattalin arzikin duniya wanda dukannin bangarorin ke fadi-tashi wajen kawar da shi.

Baya ga batun warware takun sakar na harkokin kasuwanci tsakanin EU din da Amirka, taron har wa yau zai yi kokari wajen duba batun dumamar yanayi da kuma shirin nukiliyar Iran wanda ake cigaba da kai ruwa rana a kansa.