EU na son wanzar da zaman lafiya a Libya | Labarai | DW | 16.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU na son wanzar da zaman lafiya a Libya

Ministocin harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai ta EU sun ce a shirye suke su girka wata runduna da za ta samar da tsaro da zaman lafiya a Libya.

A wani taro da suka yi dazu a birnin Brussels na kasar, ministocin suka ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen dafawa kasar ta Libya don komawa kan duga-duganta muddin ta samu gwamnatin hadin kan kasa da kowa zai amince da ita a Libya din.

Tuni dai ministocin suka ce sun umarci babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar da ta bada shawarwari kan tsare-tsare na yadda za a girka rundunar da za ta hada dakaru daga kasashen kungiyar kwatankwacin wadda ta yi aiki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya don tallafawa Libya din ta samu zaman lafiya.