EU na dari-dari kan tattaunawa da Birtaniya | Labarai | DW | 15.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU na dari-dari kan tattaunawa da Birtaniya

Shugabannin gwamnatoci da kasashen tarayyar Turai na samun rarrabuwar kawunan kan mataki na gaba na tattaunawar da suke yi da Birtaniya bayan zaben raba gardama na Brexit don raba gari tsakaninsu a 2019.

Shugabannin kasashen EU sun nemi gwamnatin Ingila ta bayyana manufofinta kafin a shiga tattaunawa kan kasuwanci tsakanin sassan biyu. Sai dai  Firayim Ministar Birtaniya Theresa May ta yi kira ga takwarorinta na kasashen 27 da su gaggauta kadamar da tattaunawa a kan dangantakar da ke tsakanin kasarta da EU bayan raba gari saboda muhimmancinsa ga makomar kasar.

A wani liyafar cin abincin dare tare da takwarorinta, May ta sake jadadda cewa bukatarta ta samar da hulda ta musamman da kasashen Turai bayan rabuwarsu da Birtaniya a karshen Maris din 2019.

 Ita dai Kungiyar tarayyar Turai ta  EU ta bukaci karin haske daga Birtaniya a kan abubuwa uku, wadanda suka hada da makomar 'yan asalin kasashen EU da ke da zama a Birtaniya, da makomar iyaka tsakanin Ireland ta Arewa da kuma lardin Ireland. Jean claude Juncker, Sakataren zartaswa na Eu ya ce "Kungiyar EU zata yi nazarin shawarwari daban-daban da aka mika mata ."