EU - Lambar Sacharow | Zamantakewa | DW | 12.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

EU - Lambar Sacharow

Tun shekarar 1988 ne kungiyar Hadin Kan Turai ke ba da kyautar lambar girmamawan ta Sacharow. Tana mika kyautar ne ga mutane ko kuma kungiyoyiin da suka dukufa wajen kare hakkin bil'Adama a duniya.

Ginin Majalisar Turai a Straßburg

Ginin Majalisar Turai a Straßburg

A kasar Cuba, tun shekara ta 2004 ne wata kungiyar mata da suka yi sutura da fararen kaya, ke taro a ko wace lahadi a birnin Havana, don yin zanga-zanga ta hannunka mai sanda, don nuna adawarsu ga tsare mazajensu da `ya`yansu da mahukuntan kasar suka yi, ba tare da zarginsu da aikata wani laifi ba. Su dai wadannan matan, sun zabi fararen tufafi ne don alamta manufarsu ta zaman lafiya da su da kuma rashin laifin wadanda da aka tsaren. A duk tsawon lokacin da suke zanga-zangar a ko wace lahadi, ba su taba ta da wata tarzoma ba. Suna jerin gwano ne a kan titin nan na Avenida Sinko da ke birnin Havana zuwa cocin Santa Rita. Kuma ba su daina ba, har saim lokacin da aka sako `yan uwan nasu.

Wannan kungiyar dai na cikin wadanda za a bai wa lambar girmamawar nan ta Sacharow ta wannan shekarar, wadda Kungiyar Hadin Kan Turai ke bayarwa a ko wace shekara. Masu fafutukar kare hakkin dan Adam, kamar lauyar nan Hauwa Ibrahim ta Najeriya, wadda ita ma za ta sami lambar ta wannan shekarar, na bayyana cewa, daukan matakai na hannunka mai sanda, su ne suka fi inganci a wannan fafutukar.

Kungiyar Hadin Kan Turai, ta ce an zabi Hauwa Ibrahim a cikin masu samun lambar girmamawan ne, saboda gagarumin nasarar da ta samu wajen kare mata da matasa da ta yi a kotunan shari’ar islama a arewacin Najeriya. Lauyar, ta yi tashe ne a lokacin shari’ar nan da aka yi wa Safiya Hussaini da Amina Lawal, wadanda aka yanke musu hukuncin kisa saboda laifin zina da aka same su da aikatawa. Ita dai lauya Hauwa Ibrahim ta cim ma nasarar ceto su ne bayan daukaka karar da ta yi a babban kotu. Game da aikin da take yi kuwa, lauyar ta bayyana cewa, an sha nuna musu wulakanci da suka da ma kwatanta su da karuwai. Bisa cewarta dai:-

„Ana zarginmu ne da nuna kyama ga shari’a, kai har ma da addinin musulunci. Wasu kuma sun ce muna watsi da jigajigan al’adunmu. Har ila yau dai, akwai ma wadanda suka kira mu karuwa.“

A lokacin da aka kaddamad da shari’ar dai, Hauwa Ibrahim ta ce ba ta da izinin bayyana a kotun, don kare wadanda ake tuhuma, saboda ita mace ce. Kuma, maza lauyoyi ne kawai ake bai wa damar bayyana gaban alkalan. Sabili da haka, abokan aikinta maza ne take turawa zuwa kotun. Amma dai tun 1999, al’amura sun sake. A halin yanzu, lauyar, mai shekaru 38 da haihuwa, na da izinin bayyana a kotu don kare wadanda ake tuhuma da aikata laifuffuka.

Daya kungiyar da za a bai wa lambar girmamawar kuma, ita ce „Reporter Sans Frontière“, kungiyar nan da ke fafutukar kare `yancin maneman labarai a duniya baki daya. Tun shekaru 30 da aka kafa ta dai, kungiyar ta yi ta kokarin cim ma sako maneman labarai da iyalansu da aka tsare a kasashe daban-daban, tana kuma taimaka wa maneman labarai da ke gudanad da ayyukansu a yankunan da ake yake-yake ko kuma rikici ya barke a cikinsu. Duk da nasarorin da kungiyar ta samu dai, ta bayyana cewa har ila yau a kasashe da dama na duniya, ana ci gaba da fatattakar maneman labarai ta hanyoyi daban-daban. Kamar yadda Katrin Evers, kakakin kungiyar a birnin Berlin ta bayyanar:-

„Matakan sun hada ne da janye lasinsin aikin maneman labaran, ko kuma habaka farashin takardun buga jaridu. Akwai kuma wasu wurare inda har ila yau ake ta afka wa maneman labarai, ana garkuwa da su, a wasu lokutan ma a halaka su. kasashe da dama dai na da nasu dabarun na angaza wa maneman labarai.“

Duk wadanda aka bai wa lambar girmamawan dai, sun sha yunkurin kare hakkin dan Adam a bangarorinsu, a wasu lokutan ma, tare da huskantar kasadar rasa rayukansu. Dukkansu dai sun nuna matukar kwazo wajen bin manufofin da suka sanya a gaba. Don yabon wannan kwazon da suka nuna ne dai kungiyar Hadin Kan Turai ta tsai da shawarar ba su wannan lambar girmamawar.

Game da tambayar da aka yi mata, ta yadda za ta yi amfani da wannan kyautar da aka ba ta, Hauwa Ibrahim ta bayyana cewa:-

„Ina ganin wannan dai kamar wata dama ce da na samu, ta mai da martani ga al’ummata, wato ta mayar mata wasu daga cikin abin da na samu daga gare ta. Ita ce dai ta ba ni damar koyar wannan sana’ar. Da can dai, ban yi tunanin cewa, wani muhimmin abu nake yi ba. Buri na ne kawai in ba da gudummawa ta, tamakar lauya, wajen inganta halin zamantakewa na dan Adam.“