EU da Rasha tsugune ba ta kare ba | Labarai | DW | 17.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU da Rasha tsugune ba ta kare ba

Ya zuwa yanzu dai an kara wata shida kan takunkumi da aka kakabawa kasar da aka tsara zai kare a watan Janairu na shekarar 2016.

Wladimir Putin und Silvio Berlusconi auf Sardinien

Wladimir Putin na Rasha

Kasashe da ke zama mambobi a kungiyar EU a ranar Laraban nan sun amince su kara wa'adin lokacin da suka tsara na sanya takunkumi kan kasar Rasha saboda kutsen da take yi a kasar Ukraine.

Ya zuwa yanzu dai an kara wata shida na wannan takunkumi, kenan zai kare a karshen watan Janairu na shekarar 2016, kamar yadda majiyar kungiyar ta nunar.

A cewar majiyar, jakadu daga kasashe mambobin wannan kungiya 28 sun cimma matsaya kan shirin kara wa'adin takunkumin tun daga watan Yuli sannan za a tura wa taron ministoci na kungiyar ta EU ranar Litinin dan su samu su rattaba hannu.