1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bunkasa cinikayya tsakanin EU da India

July 15, 2020

Kungiyar tarayyar Turai da kasar India sun kudiri aniyar shirya wata gagarumar tattaunawa a kan batun kasuwanci da zuba hannu jari

https://p.dw.com/p/3fNmN
Brüssel EU Indien Videokonferenz Modi, Michel und von der Leyen
Hoto: Reuters/Y. Herman

Manyan nahiyoyin biyu masu karfin tattalin arziki sun cimma matsayar shirya gagarumar tattaunawa a kan batun kasuwanci da zuba hannu jari bayan wani taro da suka gudanar ta kafar Internet, sai dai ba a ambaci wani abu da ya danganci batun yarjejeniyar cinikayya ba tare da shamaki ba da aka kwashe shekaru da dama ana tattaunawa a tsakaninsu.

Taron wanda ya sami jagorancin Firanministan Kasar India Narendra Modi da shugabannin tarayyar Turai Charles Michel da kuma Ursula von der Leyen ya mayar da hankali ne kan yadda za a habaka yarjejeniyar kasuwanci wanda zai samar da yanayi mai kyau na cinkayya da kuma ga masu zuba hannun jari tare da cike gibin da ake samu na samar da kayayyaki.

Kungiyar tarayyar Turai ce dai babbar abokiyar cinikayya ga kasar Indiya wanda cinikayya tsakanin bangarorin biyu ta kai dala billiyan 115.6 a shekarar 2018 zuwa 2019