EU da Birtaniya sun fara tattaunawa
June 19, 2017Talla
Jagoran tattaunawar kungiyar EU Michel Barnier da takwaransa na Britaniya David Davis sun shedawa manema labarai cewa sun shirya tattaunawar don shata yadda Britaniya za ta fice daga kungiyar baki daya.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Firaiministar Britaniyan Theresa May ta rasa gagarumar rinjaye da take da shi a majalisar dokokin kasar al'amarin da ake ganin zai iya haifarwa kasar tarnaki a tattaunawar.
Al'ummar Britaniya dai sun zabi ficewa daga kungiyar EU a zaben raba gardama da aka yi a bara.