EFCC ta sake gano makudan kudade a Legas | Siyasa | DW | 09.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

EFCC ta sake gano makudan kudade a Legas

Hukumar EFCC a Najeriya ta ce ta gano Naira biliyan 47 da kuma dala miliyan 487 da ta ke zargin mallakin tsohuwar ministar mai ta kasar ne wato Diezani Alison-Madueke wacce ke fuskantar tuhuma ta kwasar dukiyar kasa.

Wadannan makudan kuaddden da aka gano da hukumar ta EFCC ta bayyana cewa sakamako ne na bincike na kwakwafa da jami'anta suka dauki lokaci suna gudanarwa a daya daga cikin katafaren gidaje mallakar tsohuwar ministan man ta Najeriya. Baya ga kudade, EFCC din ta ce jami'anta sun kuma gano akwatuna da aka boye zinare da azarfa da tagula wadanda kudadensu miliyoyin Naira bisa ga kimar da aka yi musu.

Wannan nasara da EFCC din ta kai ga samu dai na faruwa ne kwanaki biyu bayan da wata kotu ta hallata kwace wani katafaren gida malakar tsohuwar ministar ta Najeriya wanda kudinsa ya kai sama da dalla milyan 37. Yayinda gwamnati Najeriya ke wannan kokari, al'ummar kasar na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu kan irin abinda ya kamata a ce hukumomi sun yi da wadannan kadarori da kuma kudade da aka sace daga aljihun gwamnati.

Abubuwan da ake cigaba da bankadowa na cin hanci a Najeriya dai na nuna yadda aka yi wawaso na dukiyar kasa da ya sanya a yanzu ‘yan Najeriyar ke ji a jikinsa ta hanyar koma bayan tattalin arziki da ake fadan zai sanya idon kowa ya bude a kasar don taimaka wa bankado masu halin bera a Najeriyar.

Sauti da bidiyo akan labarin