ECOWAS za ta saurari karar Sambo Dasuki | Labarai | DW | 11.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ECOWAS za ta saurari karar Sambo Dasuki

Kotun kungiyar habaka tattalin arziki ta kasashen Yammacin Afirka wato ECOWAS ta yanke shawarar fara sauraran karar da Sambo Dasuki ya shigar gabanta.

Kanal Sambo Dasuki ya shigar da karar ta hannun lauyansa a inda yake neman kotun ta bi masa hakkinsa na ci gaba da tsare shi ba tare da an yanke masa hukunci ba a Najeriya. Ana zargin tsohon mai bai wa tsohon shugaban Najeriya shawara da sama da fadi da kudin sayan makamai don yaki da Boko Haram.

Chijoke Nwoke da ke zama alkali a kotun ya ce bisa dukkan alamu batutuwan da aka kawo a gaban kotun sun nuna karara cewar wanda ake tuhuma ya na son ganin ya samu 'yancinsa.

Shi dai Sambo Dasuku na daga gaba gaba wajen samunsa da hannu dumu dumu a kan badakalar kudaden sayo makamai da suka tasarma dala biliyan biyu, a inda suka yi kashe mu raba gabanin zaben shekara ta 2015 da aka ware don yakar Boko Haram.

Tun dai lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya hau karagar mulkin kasar ya sha alwashin kakkabe cin hanci da karbar rashawa da ya yiwa kasar katutu.