Ebola: Bankin Duniya ya bawa Saliyo kudi | Labarai | DW | 03.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ebola: Bankin Duniya ya bawa Saliyo kudi

Shugaban Bankin Duniya Jim Yong Kim ya sanar da baiwa Saliyo miliyan 160 na euro don agaza mata wajen yaki da cutar Ebola da ta yi sanadin rasuwar mutane da dama.

Kim ya ce banki ya amince da mika wannan kudi ga Saliyo din ne don inganta cibiyoyi na yanki da ke yaki da Ebola da ma samar da kungiyoyi na jami'a da za su kasance cikin shirin ko ta kwana don dakile annobar a yammaci da arewacin kasar.

Baya ga wannan, babban jami'in na Bakin Duniya ya ce za a yi amfani da wani kaso na kudin don tallafawa bangaren noma na kasar da ya shiga halin ni 'yasu domin gujewa fadawa ja'ibar yunwa kazalika za a samar da aiyyukan yi ga mazauna yankunan karkara.

Kimanin mutane dubu da kusan dari shidda ne dai cutar ta Ebola ta yi ajalinsu a Saliyo yayin da wasu sama da dubu bakwai ke dauke da kwayar cutar yanzu haka.