1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTimor ta Gabas

Dubban 'yan Isra'ila na zanga-zangar adawa da gwamnati

March 31, 2024

Bayanan da ke fitowa daga Isra'ila sun nuna cewa dubban mutane za su ci gaba da jerin zanga-zanga da a wannan Lahadi , bayan wadda aka gudanar a manyan birane a ranar Asabar.

https://p.dw.com/p/4eHpJ
Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Isra'ila
Yadda ake zanga-zangar adawa da gwamnati a Isra'ilaHoto: Eyal Warshavsky/ZUMAPRESS/picture alliance

Zanga-zangar adawa da gwamnatin Isra'ila ta yi karfi a biranen Tel Aviv da kuma Kudus, daga wasu gangamin da suka dauki hankali ranar Asabar a kasar.

Zanga-zanga ce kuwa da ke zuwa yayin da ake kokarin shiga watanni shida na yaki a Zirin Gaza.

Dubban masu boren sun toshe babbar hanyar Tel Aviv suna mai bukatar da a gaggauta zabe sannan kuma a sako sama da Isra'ilawa 100 da kungiyar Hamas ke ci gaba da garkuwa da su.

Haka ma an samu daruruwan su da suka yi wa gidan Firaminista Benjamin Netanyahu da ke birnin Kudus tsinke, suna mai bai wa gwamnatinsa mai tsaurin ra'ayi laifin rashin kubutar da mutum 130 din suka yi amannar suna Zirin Gaza.

Akwai ma dai wadanda ke daukar an kashe Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da sun.

Kafofin watsa labaran Isra'ila, sun ruwaito labaran kama akalla mutum 16 daga cikin masu zanga-zangar.

Akwai kuma bayanan da ke nuna cewa masu boren za su fara jerin zanga-zanga da zai fara daga yau Lahadi a Kudus.