1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Schumer: Netanyahu ne matsalar zaman lafiya

Abdullahi Tanko Bala
March 14, 2024

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattijan Amurka Chuck Schumer ya bukaci Isra'ila ta gudanar da sabon zabe

https://p.dw.com/p/4dXJX
Chuck Schumer shugaban masu rinjaye a majalisar dattijan Amurka
Chuck Schumer shugaban masu rinjaye a majalisar dattijan AmurkaHoto: Anna Moneymaker/Getty Images

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattijan Amurka Chuck Schumer ya yi kira ga Israila ta gudanar da sabon zabe yana mai cewa ya yi imani Firaminista Benjamin Netanyahu ya kauce hanya kuma ya zama cikas ga samun zaman lafiya a yankin.

"Ya ce mutum na hudu da ke zama tarnaki ga zaman lafiya a Israila shi ne Firaminista Benjamin Netanyahu wanda sau da dama ya na mika wuya ga bukatun masu tsattsauran ra'ayi a cikin ministocinsa kamar Smorteich da Ben-Gvir da kuma yan share wuri zauna da ke gabar yamma."

Shugaban masu rinjayen a majalisar dattijan ta Amurka ya ce masalaha kadai ita ce ta kasashe biyu da za su zauna daura da juna. Ya ce hakan shi ne zai kawo  cigaba ga Israila da Falasdinawa.

Schumer shi ne Bayahude na farko mafi girman mukami a majalisar dattijan Amurka da ya yi kakkausar suka ga Netanyahu a jawabin da ya yi a zauren majalisar dattijan.