Dokar kare cin zarafin mata a Najeriya | BATUTUWA | DW | 07.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Dokar kare cin zarafin mata a Najeriya

A Najeriya shirin doka na majalisar datawa kan samar da daurin shekaru 14 ga duk wanda aka samu da cin zarafin mata a manyan makarantu da samar da kariya ga alkalai da ma'aikatan shari'a saboda matsalar garkuwa da jama'a

Wannan mataki da majalisar datawa ta Najeriya ta dauka a kan wannan matsala ta cin zarfi da ma lalata da dalibai mata da ke manyan makarantun Najeriya musamman jami'o'i sun ce mataki ne na kawar da wannan mumunan dabi'a inda wasu malaman kan yi amfani da wannan a matsayin sharadi na bai wa daliban maki a jarabwa, ko kuma su kayar da su. Ci gaba da bankado wannan matsala da ya sanya a jami'o'i da dama ta kai ga korar malaman da aka kama su dumu-dumu ya sanya mayar da murtani a kan kudurin doka da aka yi wa karatu na biyu.

Duk da tanade-tanade da dokar ta yi da ya hada da hukunta duk wani kokari na runguma ko kwarkwasa ga dalibai mata da nufin cin zarafinsu, amma ba ta hada da makarantun firamare da na sakandire ba.

A daya bangaren kuma majalisar wakilan Najeriya ta amince da kudurin da ya tanadar da samar da karin tsaro ga alkalai daga masu garkuwa da jama'a saboda yadda ake yawan sace su. Hon Sada Soli Jibia dan majalisar wakilan Najeriya ya bayyana cewa hana ne ya dace.

To sai dai lamarin ya harzuka wasu ‘yan Najeriya musamman wadanda wannan matsala ta shafe su kai tsaye, sanin cewa batun garkuwa da jama'a lamari ne da ya zama gidan kowa. Samar da doka a Najeriya dai ba matsala ba ce amma aiwatar da ita, za a saka ido a ga tasirin da wannan zai yi ko zai iya kauce wa kin hukunta wadanda ke aikata laifin abin da ke nuna tafka da warwara a daukacin lamarin.

 

Sauti da bidiyo akan labarin