Daurin rai da rai kan wadanda suka kashe jakadan Rasha | Labarai | DW | 09.03.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Daurin rai da rai kan wadanda suka kashe jakadan Rasha

Kotu a Ankara ta zartas da hukuncin daurin rai da rai kan mutanen da aka samu da laifin hannu a kisan jakadan kasar Rasha da ke Turkiyya a shekarar 2016.

Kotu a birnin Ankara, ta yanke wa mutanen biyar hukuncin daurin rai da rai ne, bayan da ta ce, ta same su da laifin hannu a kisan jakadan Rasha Andrei Karlov. Jaridar Anadolu da ake bugawa a kasar, ta ce, bayan dogon nazari, kotun ta ce, tayi amfani da hujjoji da aka gabatar a gabanta da suka nuna yadda mutum uku daga cikinsu suka taimaka wa wanda ya harba bindigar da ta halaka jakadan.


Akwai kuma wasu mutum takwas suma da aka yanke ma hukunci zaman gidan yari na shekaru tsakanin uku zuwa goma bisa laifin hannu a kitsa harin. Suna daga cikin mabiya malamin addinin kasar, Fethullah Gulen da gwamnatin Ankarar ke zargi da yunkurin yi mata juyin mulki dama son hana zaman lafiya a kasar. An dai kai hari kan jakadan, Andrei Karlov a yayin da ya ke jawabi a wani taron baje-koli a birnin Ankara, maharin yayi kabbara tare da furta kalamai na adawa da rawar da Rasha ke takawa a rikicin Siriya kafin ya bindige shi.