1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaddada daure tsofaffin sojoji a Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou YB
December 19, 2018

Kotun cour de cassastion ta daukaka kara ta yi watsi da karar da wasu manyan hafsan sojan Nijar da aka zarga da yunkurin juyin mulki a shekarar 2015 suka shigar don kalubalantar hukuncin da kotun soja ta yanke masu.

https://p.dw.com/p/3AO7J
Verfassungsgericht in Niamey Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Kotun ta ce hukuncin da aka yanke wa Janar Salou Souleymane tsohon hafsan hafsoshin sojan sama na kasar na zama gidan yari har tsawon wa'adin shekaru 15 da kotun sojan ta yi a baya na nan daram, biyo bayan zarginsa da zaman kashin bayan yunkurin juyin mulki a tsakiyar watan Disamban shekarar 2015.

Kana kuma kotun ta kara jaddada hukuncin daurin shekaru ga Laftanal Kanal Ousmane Awal Hambali da Yandou Souleymane da ke a matsayin da ga Janar Salou Souleyman din na tsawon shekaru 10, da shekaru biyar a gidan wakafi. Tun da fari dai lauyoyin da ke kare hafsoshin sojan sun bayyana cewar da akwai wasu ka'idojin kundin tsarin mulki da kotun sojan ke takawa, saboda hakan a dage zaman kotun, bukatun da kotunan biyu duka suka yi watsi da su. A farkon wannan shekarar ne dai aka gabatar da zaman kotun shekaru biyu bayan daure manyan hafsoshin sojan da ake zargi da yunkurin juyin mulki.