1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Darasin Rayuwa:Nishadi don debe kewa

Abdul-raheem Hassan
April 9, 2021

Cutar corona ta ki karewa a wasu kasashen da ake da karancin fahimta ko ma yarda da cutar, yayin da wasu kasashe cutar ke cigaba da barazana. Kasashe kamar Najeriya, an shiga yanayin dokar kulla mai tsanani a baya.

https://p.dw.com/p/3rlH5
Nigeria Flughafen Abuja | Coronavirus | Wiedereröffnung
Hoto: DW/U. Abubakar Idris

An dai tafka muhawara mai zafi a kasashen Afirka a loakcin zuwan cutar corona kan tasirin dokokin kulla da wasu kasashe suka dauka na hana fita kamar yadda wasu ksashen Turai suka yi. Da dama an yarda kullen ya taimaka wajen yaki da yaduwar cutar tsakanin jama'a ta hanyar takaita cudanya, sai dai wasu da dama sun ga illar haka na yada yunwa ke barazana idan mutane ba su fita neman abinci ba. Baya ga wannan, zama haka kawai, ba wutar lantarki babu damar a shiga yanar gizo don bincike ko hira ta shafukan sada zumunta, ya tsananta rayuwa a zamanin kullen, wanda wasu ke ganin ya haddasa musu matsalar yawan tunani da ke shafar kwakwalwa. Jihar Kaduna na cikin jihohin da suka tsananta dokar kulle a Najeriya, to ko ya al'umma suka samar wa kansu mafita na saukin rayuwa? Wannan shi ne batun da Drasin Rayuwa na (10-04-21) ya tattauna a kai.