Tusk ya gargadi Turan kan dangantaka da Amirka
June 27, 2018Talla
Shugaban hukumar tarayyar Turai Donald Tusk ya ja hankalin shugabannin kasashen kungiyar tarayyar cewa su yi shirin fuskantar yanayi mafi muni a dangantakar kungiyar tarayyar Turai da Amirka.
Ya baiyana hakan ne a wata wasika da ya aike wa shugabannin kasashen Turan wadanda za su halarci taron kolin kungiyar da zai gudana a ranaikun Alhamis da Juma’a.
Tusk yace manufofin Trump na kara cin karo da akidun Kungiyar tarayyar Turai.
Batun ‘yan gudun hijira da na tattalin arziki su ne za su kasance kan gaba a jadawalin taron.