Saboda tasirin shafukan sada zumunta ne musamman tsakanin matasa, shirin ya karkata akalarsa kan makon shafukan sadarwar da aka bude a birnin Legas da ke kudancin Najeriya.
Sama da mutane biliya hudu ke mu'amala da yanar gizo a duniya, kuma Indiya ce ke kan gaba da kusan mutane miliyan 54.
Kuma a shafukan sada zumunta Facebook ya yi zarra musamman a nahiyar Afirka, da kusan mutane miliyan 120 ke amfani da shi, kuma na kimanin kashi 80 cikin 100 an fi yin Facebook din ta waya.