1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambarwar tsige minista a Nijar

Salissou Boukari MA
February 1, 2019

Bayan sanar da tsige ministan kudi na Jamhuriyar Nijar Hassoumi Masaoudou ‘yan kasa da sauran masharahanta na ci gaba da bayyana ra’ayoyi kan matakin na ba zata.

https://p.dw.com/p/3CZvB
UN-Klimakonferenz 2017 in Bonn | Mahamadou Issoufou, Präsident Niger
Hoto: Getty Images/AFP/P. Stollarz

Jama’a na ci gaba da tafka muhawara kan wannan batu na tsige ministan kudi na Jamhuriyar Nijar Hasoumi Masaoudou, inda aka maye gurbinsa da tsohon ma’aikacin babban bankin kasashen yammacin Afirka, malam Amadou Diop.

Shi dai wannan ministan da aka tsige Hasoumi Masaoudou, mutum ne da ake yi wa kallon mai tsaurin ra’ayi musmamman ma idan aka dubi yanda aka sha gwagwarmaya da kungiyoyin fararan hula masu yaki da tsadar rayuwa a kasar, da ma yadda ake ganin ya yi amfani da mukaminshi wajen rufe wasu kafafen yada labarai, amma duk da haka wasu na jinjina masa kan matakan da yake dauka wadanda ake ganin sai da mutane irinsu kasa za ta iya samun ci gaba.

A halin yanzu dai kallo da kunnuwa sun karkata ya zuwa bangaren gwamnatin ta Jamhuriyar Nijar zuwa daren wannan Juma‘a a ji wani ko wasu matakan da za su biyo tsigewar.