Dakon ministoci a Tarayyar Najeriya | Labarai | DW | 30.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakon ministoci a Tarayyar Najeriya

A wannan Larabar ne ake sa ran gwamnati a Tarayyar Najeriya za ta gabatar da sunayen ministoci a gaban majalisar dokokin kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Tsahon watannin biyar ke nan da rantsar da sabuwar gwamnatin ta Buhari sai dai har kawo yanzu babu minista koda guda daya da aka nada. Rahotanni sun nunar da cewa Shugaba Buhari ne zai kasance ministan man fetur na kasar kamar yadda kakakinsa Garba Shehu ya tabbatar. A cewar janar manaja a fannin ci-gaba da kuma yada labarai na kamfanin mai na Shell a Tarayyar Najeriyar Igo Weli, in har hakan ta kasance su na maraba, inda ya ce:

"Mu rawar da za mu taka ita ce mu bawa gwamnati hadin kai saboda mu dama abokan huldarta ne. Mun amince da sabuwar gwamnatin kasancewar ta yi kokari tun bayan da aka rantsar da ita, a dangane da haka za mu yi aiki tare da gwamnatin da ma duka 'yan Najeriya."

Sai dai acewar wani mai fashin baki Malte Liewerscheidt kasancewar Buhari a matsayin ministan man fetur zai taimaka matuka wajen kawo gyara a fannin, sai dai ya ce dole sai an yi taka tsan-tsan.