Dakarun Siriya sun kaddamar da farmaki a Aleppo | Labarai | DW | 16.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Siriya sun kaddamar da farmaki a Aleppo

Sojojin gwamnatin Siriya sun kaddamakar da farmaki samakaon samun tallafi daga jiragen saman yaki na kasar Rasha.

Dakarun kasar Siriya da ke samun rakiyar jiragen saman yaki na Rasha sun kaddamar da farmaki kan 'yan tawaye a kudancin birnin Aleppo da ke zama birni na biyu mafi girma a kasar. Wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta ce dakarun gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad ta kwace iko da wasu garuru biyu bayan jiragen saman yakin na rasha sun kai farmaki.

A wani labarin bincike kwararru na Majalisar Dinkin Duniya ya gano magoya bayan kungiyar IS da ke ikirarin neman kafa daular Islama suna bayar da kimanin dala dubu-10 domin samun masu Jihadi a kasashen Siriya da kuma Iraki. Galibin mayaka 'yan kasashen wajen sun fito ne daga Beljiyam.