Dakarun Najeriya sun sake yin nasara | Labarai | DW | 17.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Najeriya sun sake yin nasara

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta yi nasarar fatattakar 'yan Kungiyar Boko Haram daga akasarin garuruwan yakin Arewa maso gabashin kasar

A lokacin da ya ke yi wa manaima labarai bayani a birnin Abuja, hafsan hafsoshin sojojin Najeriya Janar Kenneth Minimah ya ce kananan hukumomi uku ne kawai ke hannun masu tayar da kayar bayan a halin yanzu, daga cikin kananan hukumomi sama da 20 na Arewa maso gabashin Najeriya da suka fada hannun 'ya'yan Boko Haram.

Babu dai wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari na rundunar sojojin Najeriya. Sai dai kuma ta saba bayar da bayannan da ke karyata kansu daga bisani. Idan dai za a iya tunawa cibiyoyin da ke kula da tsaro a Najeriya sun nemi hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta dage zaben gama gari daga watan Fabrairu zuwa Maris don su samu damar murkushe 'yan Boko Haram a cikin tsukin wannan lokaci.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Pinado Abdu Waba

  • Kwanan wata 17.03.2015